Jam’iyyun Adawa Na Ci Gaba Da Fama Da Shari’o’i A Gaban Kotuna



Rahotanni na bayyana cewa yawan shari’o’i da ke karuwa da suka shafi jam’iyyun adawa a Nijeriya na jefa shakku kan damar su gabanin zaben 2027, yayin da shirye-shiryen siyasa suka fara kakama kafin yadda ake tsammani da kuma yadda doka ta tanada.

Wadannan rikice-rikicen sun kara zurfafa rabuwar kan a cikin jam’iyyun adawa, sannan suna barazana ga hadin kan jam’iyya da kuma tsarin dimokuradiyya baki daya.

Jam’iyyar PDP ta kasace babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya tun daga 2015, ita ce wadda abin ya fi shafa. Jerin hukunci daga kotu da ke karo da juna ya kai ga hargitsi a babban ofishin jam’iyyar a ranar Talata, wanda lamarin ya haifar da ‘ya kallo da dama tare da saka alamar tamaya ko jam’iyyar za ta ci gaba da dorewa iko kuma za ta mutu.

Yayin da wasu masana suke ba da shawara cewa PDP na kan hanyar samun kwanciyar hankali bayan babban taronta na kasa, wanda aka gudanar duk da umarnin kotu biyu da suka dakatar da shi, har yanzu akwai sauran rina a kaba, inda bangaren ministan Abuja, Nyesom Wike ke jagoranta ya yi watsi da taron sakamon korar sa da aka yi, wanda hakan na iya neman daukar matakin shari’a.

An sami manyan shari’u guda uku game da taron PDP, guda biyu a babban kotun tarayya a Abuja da guda daya a babban kotun Jihar Oyo a Ibadan. A Abuja, reshen da ke adawa da taron, wanda ya kunshi mabiyan Wike da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, sun sami hukuncin dakatar da taron, inda daya ya bayyana cewa an hana Lamido saya fom din takarar shugaban jam’iyyar na kasa.

A babban kotun Jihar Oyo, a cikin karar da magoya bayan gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde suka shigar, ta amince da taron, duk da cewa har yanzu ba a yanke hukunci a mahangar shari’a ba. Bangaren Makinde da gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammed sun goyi bayan Kabiru Tanimu Turaki (SAN) a matsayin sabon shugaban jam’iyyar tare da goyon bayan kwamitin amintattu karkashin tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara.

Kazalika, jam’iyyar LP, wadda ta zo ta uku a zaben shugaban kasa na 2023, ta shiga rikicin shugabanci mai tsawo. Bangarori masu hamayya sun yi amfani da hukuncin kotu daban-daban don tabbatar da sahihancinsu, har ma suna kin bin hukuncin kotun koli wajen warware rigingimun. Masana na gargadi cewa wannan ci gaba da rikici na iya raunana damar jam’iyyar wajen shirya zaben fid da gwani da kuma fitar da ‘yan takara masu inganci a shekarar 2027.

Ita ma sabuwar jam’iyyar NNPP, wadda ta zo ta hudu a 2023, na fuskantar irin wannan rikici. Hukuce-hukuci kotuna da dama sun amince da rassan daban-daban, wanda ya sa ayyukan jam’iyyar sun tsaya cak.

Jam’iyyar ADC, wadda yanzu ke karkashin jagorancin hadin gwiwar ‘yan adawa, tana fama da rikice-rikicen shari’a na cikin gida. Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dumebi Kachikwu, ya kalubalanci hadi gwiwar jam’iyyar a gaba kotu, inda har yanzu ba yanke hukunci ba, abin da ke nuna irin mawuyaci hali da jam’iyyar za ta iya fadawa kafin 2027.

A farkon wannan shekara ce, kotun koli ta yanke hukunci da nufin warware rikice-rikice na cikin gida a cikin PDP da LP, amma lamarin ya ci tura. Kotun kolin ta jaddada cewa al’amuran cikin gida na jam’iyya, ciki har da neman takarar shugabanci, galibi suna karkashin kundin tsarin jam’iyya kuma ba sa karkashin hukuncin kotu, sai in har an take hakkokin Dan’adam. Duk da haka, hukunce-hukunce masu karo da juna na kananan kotuna sun raunana wannan ka’ida, inda masana shari’a suka danganta hakan ga juya hukunci a kotuna.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *