Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu

[ad_1]



Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101.

A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi.

Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.

“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito da hikima. A matsayinsa na mai wa’azi kuma babban mai fassarar Alƙur’ani mai tsarki, ya kasance mai kira ga zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.

Ya tuna da albarka da ya samu daga marigayin a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2023.

Shugaban Ƙasa ya miƙa ta’aziyya ga almajiran malamin a faɗin Najeriya da wajen ƙasar, yana mai kira da su dawwamar da sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, tsoron Allah da kyautatawa ɗan adam.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *