’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, tare da ’yan majalisar 15 sun sauya sheka daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa APC.
A saifyar Litinin ne Rt Hon. Kizito Bonzena ya gabatar da takardarsa ta ficewa daga PDP tare da sauran mambobin zuwa APC.
Ya bayyana cewa da sauyin shekar tasu, yanzu APC ce ke da daukacin kujeru 24 da ke Majalisar Dokokin Jihar Taraba.
Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Gwamnan Jihar Taraba, Kefas ya sanar da shirinsa na komawa APC daga PDP.
Sauran mambobin majalisar da suka sauya sheka sun hada da Mataimakin Shugaban Malisar, Hamman Adama Abdullai (Bali 2) da Shugaban Masu Rinjaye, Jethro Yakubu (Wukari 1). Sauran sun hada da Tafarki Eneme (Kurmi ); Akila Nuhu (Lau ); Musa Chul (Gassol 1); da Josiah Yaro (Wukari 2).
Akwai kuma Tanko Yusuf (Takum 1), Veronica Alhassan (Bali 1), Anas Shuaibu (Karim Lamido 2), Nelson Len (Nguroje), Umar Adamu (Jalingo 1), Joseph Kassong (Yorro), John Lamba (Takum 2), Happy Shonruba (Ardo-Kola) da kuma Zakari Sanusi (Ibi Constituency).
Da yake sanar da sauyin shekar tasu, shugaban majalisar ya bayyana cewa sun yi hakan ne saboda bukatar al’umma ba don bukatar kansu ba.
Tsohon Shugaan Malisar Dokokin Jihar, Peter Diah, ya yi maraba da su a APC.