Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi
[ad_1]
’Yan ta’addan Lakurawa sun kai hari sansanin Hukumar Kwastam da ke Maje, a Ƙaramar Hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi, inda suka kashe wani jami’i guda ɗaya.
Wani mazaunin yankin ya ce ’yan ta’addan sun zo da yawa, inda suka fara harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, sannan suka ƙone sansanin jami’an kwastam.
Ya ce, “Lakurawa sun zo da yawa, suna harbe-harbe ta ko ina. Sun ƙone sansanin kwastam tare da kashe wani jami’i.”
Mai magana da yawun hukumar Kwastam a Jihar Kebbi, Muhammad Tajudeen, ya tabbatar da faruwar harin.
Ya ce jami’an hukumar suna asibiti suna jiran rahoton likita don tabbatar da ko jami’in da aka harba ya rasu.
Ya ce: “Harin ya faru da gaske, amma likita ne zai tabbatar ko jami’in ya rasu ko akasin haka. Muna jiran rahoton likita kafin mu fitar da cikakken bayani.”
Wannan harin na zuwa ne mako guda bayan wasu ’yan ta’adda sun sace mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Muhammad Sama’ila Bagudo.
Mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya yi sanadin lalacewar kayayyakin kwastam a sansanin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link