Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya fice daga jam’iyyar PDP ne, saboda ya hana shi lalata jam’iyyar.
Yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, Wike ya bayyana cewa Atiku ba ya cikin mutanen da suka taɓa zama masu aminci ko jajircewa ga jam’iyyar.
“Atiku bai da wani zaɓi face barin jam’iyyar, domin yana son amfani da PDP don cimma burinsa,” in ji Wike.
“Amma ya san muddin ina cikin jam’iyyar, ba zai iya yin hakan ba.”
Wike ya zargi Atiku da wasu jiga-jigan jam’iyyar da lalata ta, inda ya bayyana cewa Atiku ya sha ficewa daga PDP sannan ya koma.
Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.”