Abba ya umarci a riƙa gudanar da taron tsaro a ƙananan hukumomin Kano
[ad_1]
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci shugabannin dukkan ƙananan hukumomin jihar da su riƙa gudanar da tarukan tsaro akai-akai domin ƙarfafa zaman lafiya da kariyar rayuka da dukiyoyin al’umma.
A cewar wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba ya jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri da musayar su a tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin magance matsalolin da ke addabar yankuna.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rahotannin hare-haren ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin da ke kan iyaka da Jihar Katsina da sauran yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Gwamnan ya bayyana ƙananan hukumomin Shanono, Tsanyawa, Tudun Wada, Doguwa da Gwarzo a matsayin wuraren da ke buƙatar kulawa ta musamman saboda barazanar tsaro da ke ci gaba da tasowa a can.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da haɗin gwiwa da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an hana ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifi samun mafaka a cikin jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne dakarun Rundunar Sojin Najeriya suka daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan.
Bayanai sun ce sojojin ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwa ta Operation MESA sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar, bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link