Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

[ad_1]


Rundunar Sojojin Nijeriya (AFN) za ta gudanar da bikin kammala aiki na tsohon Shugaban Tsaron Ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a ranar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025, domin girmama ayyukan da ya gudanar a lokacin hidimarsa.

A cewar sanarwar da shalƙwatar tsaro ta ƙasa (Dhq) ta fitar a ranar Alhamis, an shirya bikin Jan hankali ɗin ne da ƙarfe 09:00 na safe, inda manyan hafsoshin Soja, da jami’an gwamnati da ƴan uwa za su halarta. Wannan biki na nuni da kammala aikin Soja a matakin ƙoli, kuma yana ɗaya daga cikin manyan al’adun da ake yi wa manyan jami’an da suka yi aiki da ƙwarewa da sadaukarwa.

Janar Musa ya yi aikin Soja na tsawon shekaru masu yawa, kuma ya yi shugabanci a matsayin Shugaban Tsaron Ƙasa daga Yuni 2023 zuwa Oktoba 2025. A wannan lokaci, ya jagoranci manyan hare-haren yaƙi da ta’addanci tare da ƙarfafa hulɗar haɗin gwuiwa tsakanin sassan Sojojin Nijeriya.

A ranar 24 ga Oktoba, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sabon tsarin jagorancin rundunar Soja, inda ya naɗa Manjo Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Shugaban Tsaro, wanda hakan ya kawo ƙarshen wa’adin Janar Musa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *