Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba



Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya soki Gwamnatin Tarayya saboda ci gaba da karɓo bashi bayan cire tallafin man fetur.

Da yake jawabi a wajen taron shugabanci a Abuja, Sanusi, ya ce cire tallafin man fetur an yi shi ne domin gwamnati ta samu ƙarin kuɗaɗen shiga, amma ci gaba da karɓo bashi bayan haka ya lalata manufar.

“Idan ka daina biyan tallafi amma ka ci gaba da ciyo bashi, hakan tamkar ka rufe rami ne ka kuma tona wani,” in ji shi.

“Babban abin da ya kamata yanzu shi ne yadda gwamnati ke kashe kuɗin da aka ajiye da kuma  amfani da su yadda ya dace.”

Sanusi ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa cire tallafin da kuma daidaita farashin musayar kuɗi, amma ya gargaɗi gwamnati cewa waɗannan gyare-gyare ba za su yi tasiri ba idan babu gaskiya da tsari wajen kashe kuɗi.

“Ba za mu ci gaba da ɓata kuɗi a kan abubuwan banza ba, kamar yawan ministoci, sayen motocin gwamnati, da ma’aikatan da ke yi wa shugabanni hidima.

“Idan muna samun ƙarin kuɗi amma muna kashe su ba daidai ba, to duk ci gaban da muka samu ba zai yi tasiri ba,” in ji shi.

Tsohon gwamnan CBN ɗin ya ce matsalolin tattalin arziƙin Nijeriya sun samo asali ne shekaru da dama.

Ya shawarci shugabanni su riƙa sauraron masu faɗa musu gaskiya maimakon waɗanda ke yabonsu kawai.

Ya kuma tunatar da ‘yan Nijeriya cewa da an cire tallafin man fetur tun wuri da ha rage wahalar da ake ciki yanzu, amma gwamnatocin baya sun kasa samun ƙarfin gwiwar yin hakan.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *