Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35
[ad_1]
Majalisar Tarayya, ta amince da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karɓo rancen dala biliyan 2.35 domin cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025.
Dukkanin Mjalisun sun amince da buƙatar ne a ranar Laraba, bayan sun duba rahoton kwamitin karɓar basussuka na cikin gida da na waje.
Haka kuma, majalisar ta amince da buƙatar Tinubu na fitar da dala miliyan 500 domin samar da muhimman ayyuka kamar faɗaɗa hanyoyin samun kuɗi ga ƙasar nan.
A cikin wasiƙar da ya aike wa majalisar tun a farkon watan nan, Shugaba Tinubu, ya bayyana cewa neman rancen ya zama dole domin aiwatar da kasafin kuɗin 2025.
Kasafin wanda ya ƙunshi Naira tiriliyan 9.28 na nufin cike giɓin da ake da shi a kasafin 2025.
Ya ce hakan zai taimaka wajen kauce wa kasa biyan bashi da kuma bin inganta ƙa’idojin kasuwar hada-hadar bashi ta duniya.
“Jimillar kuɗin da za a nema daga waje; dala biliyan 1.229 na sabon rance da dala biliyan 1.118 na sake biyan tsohon bashi zai kai dala biliyan 2.347,” in ji wasiƙar.
’Yan majalisa sun bayyana cewa rancen zai taimaka wa gwamnati ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa da kuma daidaita tattalin arziƙi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link