Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama — Dasuki
[ad_1]
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal, Abdussamad Dasuki, ya ce ba zai tsaya takara a zaɓen 2027 ba.
Dasuki, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin bai wa matasan Najeriya damar shiga harkokin mulki.
Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2011 yake majalisar dokoki, kuma yana ganin zai fi dacewa idan aka bai wa matasa dama a dimokuraɗiyya.
“Najeriyar da muke mafarki za ta tabbata ne kawai idan mun yi sadaukarwa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa bayan tuntuɓar iyalansa da jagororinsa, ya yanke shawarar bai zai sake tsayawa takara ba don ya gaji ba, sai don bai wa wasu dama.
Dasuki dai shi ne shugaban riƙon kwarya na ƙungiyar ‘Future Is Now Project’, ƙungiyar da ke fafutukar ganin an dama da matasa a harkokin siyasa.
An ƙaddamarda ƙungiyar a ranar 1 ga watan Oktoba, 2025 a Abuja.
Ƙungiyar ta buƙaci cewa a zaɓen 2027, kashi 70 cikin 100 na kujerun majalisar wakilai su kasance a hannun matasa ’yan kasa da shekaru 40.
Ya ce ko da yake shi ma matashi ne duk da ya haura shekaru 40, don haka dole ya gwada misali da kansa.
“Idan muna son ganin matasa sun jagoranci ƙasar nan, dole mu nuna hakan a aikace, Wannan ita ce sadaukarwa. Idan na matsa gefe sabbin jagorori za su fito,” in ji shi.
Shawarar Dasuki ta zama abun a yaba, a siyasar Najeriya, domin ba kasafai ake samun ’yan siyasa suna hakura da kujerunsu don raɗin kansu ba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link