An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato

[ad_1]



Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan manoman da suke aikin girbin amfanin gona a yankin Mbor na masarautar Mushere na Ƙaramar hukumar Bokkos a Jihar Filato, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu biyu a ranar Laraba da yamma.

Shugaban Ƙungiyar matasan Mushere, Kopmut Monday ne ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin a ranar Alhamis.

A cewar shugaban matasan, ’yan bindigar sun kai farmaki wurin ne inda suka buɗe wuta kan manoman da ke cikin aikin girbin amfanin gona, inda ya ce manoman sun tsere domin tsira da rayukansu.

Shugaban ya zargi makiyaya da kai wa mambobinsu hari, inda ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin “mazauna garin Rongjing ne a jiya da yamma sun kai wa ’yan ƙungiyarmu hari a yankin Mbor a lokacin da suke girbin amfanin gona, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku da jikkata mutum biyu da harbin bindiga. Waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.

Monday yya ƙara da cewa, al’ummar yankin suka sha fama da irin wannan hari a ranar 26 ga watan Mayu an kashe mutane bakwai.

Ya ce “lamarin baya-bayan nan wani mummunan al’amari da ya faru a watan Mayu, wanda ya yi sanadin kisan mutane bakwai, da jikkata wasu da kuma ƙona gidaje da dama ciki har da coci guda biyu.”

Monday ya kuma bayyana cewa, al’ummar da aka kai wa harin baya-bayan nan, sun yi kira ga jami’an tsaro da su tura isassun ma’aikata don dawo da zaman lafiya a yankin saboda mazauna yankin ba za su iya gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *