An kashe makiyaya 4, an jikkata wani a Filato
An kashe makiyaya huɗu tare da jikkata wani a ƙauyen Fili, da ke yankin Doemak, a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan a Jihar Filato.
Rahotanni daga yankin sun ce an kai musu hari ne lokacin da suke tsaka da kiwo.
Sakataren kuɗi na Ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) a Qua’an Pan, Saeedu Abdurrahman, ya tabbatar da lamarin.
Ya ce ’yan bindigar sun kashe makiyayan amma ba su sace shanunsu ba.
Ya ƙara da cewa lokacin da ake binne waɗanda suka rasu, ’yan bindigar sun sake kai wani harin, amma jami’an tsaro sun daƙile harin.
Ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su, Shanono Muhammad, ya ce, “An kashe makiyaya huɗu, ciki har da ƙaramin yaro da ya tafi koyon kiwon shanu.
’An kashe su ne da yammacin ranar Talata yayin da suke kiwo.”
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mai magana da yawun Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, bai yi ƙarin haske kan harin ba.