DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa ’yan bindiga makamai a Kaduna




Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama wasu mutum uku da ake zargi da sayar da wa ’yan bindiga makamai da harsasai a Jihar Kaduna.

An kama su ne bayan wani samame da jami’an DSS suka kai a ƙananan hukumomin Igabi da Kachia.

An kama ɗaya daga cikinsu mai shekaru 30, a kan titin Nnamdi Azikiwe Bypass da ke Igabi.

An gano bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, bindigar PKT guda ɗaya, harsasai sama da 200.

Sauran mutum biyu kuma an kama su ne a ƙauyen Doka da ke Ƙaramar Hukumar Kachia, a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

An kama su suna ƙoƙarin yi wa ’yan bindiga safarar AK-47 guda uku a cikin wata mota ƙirar Volkswagen Golf.

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yaba wa hukumar DSS bisa wannan nasara, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta bar wani ɗan ta’adda ko mai aikata laifi ya samu mafaka a jihar ba.

Ta bakin Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Barista Sule Shuaibu, gwamnan ya kuma gode wa Shugaba Bola Tinubu da Darakta-Janar na DSS bisa goyon bayan da suke bai wa tsaro a jihar.

Ya ce tsarin zaman lafiya da gwamnatinsa ta ƙirƙiro wanda ya haɗa da tattaunawa da haɗin kai a tsakanin al’umma ya taimaka wajen rage laifuka a faɗin jihar.

Ya gargaɗi masu aikata laifi da su daina ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Hukumar DSS ta ce tana gudanar da bincike a kan waɗanda ta kama, kuma za ta tabbatar da cewa an hukunta su.

Hakazalika, ta jaddada ƙudirinta na daƙile safarar makamai a Jihar Kaduna.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *