Gwamnatin Borno rufe makarantun jihar saboda rigakafin ƙyanda da Polio

[ad_1]



Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire ta Jihar Borno ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Firamare da Sakandare na gwamnati da masu zaman kansu na tsawon kwanaki biyu domin gudanar da aikin rigakafin cututtukan ƙyanda da shan inna.

Sanarwar umarnin rufe makarantun ta fito ne daga ofishin Kwamishinan Ma’aikatar, a ranar Talata, a birnin Maiduguri.

A cewar sanarwar, za a rufe makarantun daga ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, zuwa Juma’a, 24 ga watan Oktoba, 2025.

An kuma umarci dukkan makarantun da su ci gaba da ayyukansu daga Litinin, 27 ga Oktoba, 2025, kamar yadda aka saba.

An bayyana cewa rufe makarantun na da nasaba da Ranar Rigakafi ta Kasa na shekarar 2025, wanda Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Jinƙai ta Jihar Borno ta shirya.

Sanarwar ta ce aikin rigakafin zai shafi yara masu watanni 9 zuwa shekaru 14 domin rigakafin ƙyanda (Rubella), sai shekaru 0 zuwa watanni 59 domin rigakafin shan inna (Polio).

Gwamnatin ta bukaci dukkan shugabannin makarantu da sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar da su tabbatar da bin wannan umarni na rufe makarantu na tsawon kwanaki biyu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *