Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU
Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin mako huɗu domin ta kammala tattaunawa da ƙungiyoyin ma’aikata na manyan makarantu ko kuma ta fuskanci yajin aikin ƙasa baki ɗaya daga dukkan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta.
Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero, ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, inda ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar yin aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyoyin ilimi don tabbatar da biyan hakkokin da aka amince da su, da kuma inganta kuɗin gudanarwa da albashi a jami’o’i, kwalejoji da sauran cibiyoyin ilimi.
Ajaero ya ce NLC ba za ta sake amincewa da gwamnatin da ke turo wakilai masu halartar tarurruka ba tare da ikon yanke hukunci ba, yana mai cewa wannan ɗabi’a ta jima tana dagula lamari tsakanin gwamnati da ASUU. Ya jaddada cewa duk wata ganawa da gwamnati daga yanzu sai ta haifar da mataki na ainihi, ba Alƙawurran banza ba.
Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan ci gaba da rashin biyan haƙƙoƙin malamai, da rashin aiwatar da yarjejeniyoyi, da kuma ƙarancin kuɗin gyaran makarantu, wanda ke ƙara jefa harkar ilimi cikin ruɗani. Haka kuma, ƙungiyoyin NASU da SSANU sun sake yin barazanar yajin aiki saboda gwamnati ta kasa cika Alƙawurran da aka yi musu tun da daɗewa.
Ajaero ya gargadi gwamnati da cewa idan ta gaza magance matsalolin cikin mako huɗu, NLC za ta tsunduma cikin yajin aikin ƙasa baki ɗaya, wanda zai haɗa dukkan ƙungiyoyin ma’aikata a faɗin ƙasar. Ya kuma ce daga yanzu, “babu aiki idan babu albashi”, yana mai cewa lokaci ya wuce da gwamnati ke karya yarjejeniya sannan ta hukunta ma’aikata da aka tauye musu haƙƙoƙi.