An tsinci gawar wata mata da aka yi wa kisan gilla a Yobe

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta gano gawar wata mata mai suna Falmata Abubakar, mai kimanin shekaru 45, wadda aka yi wa kisan gilla a garin Gashuwa, kusa da Jami’ar Tarayya Gashuwa (FUGA), a Ƙaramar Hukumar Bade.

Rundunar ta samu labarin ne da safiyar ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba 2025, misalin ƙarfe 7 na safe.

Wani mutum mai suna Yusuf Sarkin Baka, mazaunin unguwar Sabon Daula ne, ya gano gawar a kusa da jami’ar.

Bayan samun rahoton, ’yan sanda daga ofishin Gashuwa sun ziyarci wajen, inda suka tabbtar marigayiyar mazauniyar Abasha, unguwar Sarkin Hausawa a Gashuwa.

An same ta sanye da baƙin hijabi.

An kai gawarta Asibitin Ƙwararru na Gashuwa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

Daga baya sun miƙa wa iyalanta gawar domin yi mata jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.

Bincike ya nuna cewa, an jefar da gawar matar ne kilomita biyu daga gidanta.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya tabbatar da cewa rundunar za yi bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin.

Ya kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa rundunar haɗin kai wajen gano masu hannu a lamarin.

Rundunar ta jaddada ƙudirinta na kare rayuka da dukiyoyi, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *