Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji

[ad_1]



Tsohon Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya ce bai yi murabus daga muƙaminsa ba saboda yana da laifi.

Nnaji, ya yi murabus ne a ranar Talata bayan cece-ku-ce ya karaɗe kafafen watsa labarai tambaya kan sahihancin takardun karatunsa.

Rahoton da jaridar PREMIUM TIMES ta wallafa ya nuna cewa Jami’ar Nsukka (UNN), ta ƙaryata bai wa Nnaji takardar shaidar kammala digir a jami’ar.

Jami’ar ta ce Nnaji ya fara karatu a makarantar a shekarar 1981, amma bai kammala karatunsa ba kuma ba a ba shi shaidar kammala digiri ba.

Sai dai a wata sanarwa da Nnaji ya fitar da kansa, ya ce sun ɓata masa suna da shafe tsawon shekaru ya karewa ta hanyar aiki tuƙuru da gaskiya.

Ya ce: “Bayan tunani mai zurfi da shawara da iyalina da abokaina suka ba ni, na yanke shawarar yin murabus daga muƙamina na Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha.

“Wannan hukunci ba don na aikata laifi ba ne, face saboda ina son kare martabar ma’aikatar da kuma barin shari’a ta bi tafarkin da ya dace.”

Nnaji, ya ƙara da cewa an yi amfani da siyasa wajen ɓata masa suna ta hanyar yaɗa ƙarya.

“Waɗannan ƙarairayi sun min ciwo, sun sanya cikin damuwa, kuma sun fara zama cikas ga ayyukan ma’aikatar da kuma shirin ‘Renewed Hope’ na Shugaba Tinubu,” in ji shi.

Ya jaddada cewa ya yi murabus ne saboda kare ƙa’idar aiki da mutunci, ba saboda yana da laifi ba, inda ya tabbatar da cewa gaskiya za ta yi halinta.

Nnaji, ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, saboda ba shi damar yin aiki a gwamnatinsa, kuma ya ce zai ci gaba da goyon bayan shugaban wajen gina Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *