Fira Ministan Faransa ya yi murabus kwana guda bayan kafa gwamnati

[ad_1]



Firaministan ƙasar Faransa, Sebastien Lecornu, ya yi murabus daga muƙaminsa kwana guda bayan ya kafa gwamnatinsa.

Fira Minista Sebastien Lecournu ya sanar da ajiye mukaminsa ne a safiyar Litinin ɗin nan bayan ya yi wata da Shugaba Emmanuel Macron.

Ya yi murabus ne washegarin da ya kafa majalisar ministocinsa domin tafiyar da gwamnati, kuma ƙasa da wata guda bayan Shugaba Macron ya naɗa shi a kujerar.

A jiya  Lahadi ne ya sanar da sunayen mambobin sabuwar majalisar ministocinsa inda ya naɗa sabbin muƙamai, amma ya bar wasu da dama a kan kujerunsu, lamarin da bai yi wa ’yan adawa daɗi ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP) ya ruwaito cewa, sanarwar ajiye aikin ta zo e a yayin da ake sa ran a yau Litinin Lecornu, wanda tsohon ministan tsaron Faransa ne, zai jagoranci zaman majalisar ministocinsa ta farko.

Kawo yanzu ahi ne minista na biyar da Macron ke naɗawa cikin shekaru biyu a yayin da Faransa ke fuskantar gagarumar dambarwar siyasa.

Fadar shugaban ƙasar Faransa ta sanar a safiyar yau Litinin cewa Shugaba Macron ya amince da murabus ɗin babban na hannun daman nasa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *