Kwamitin gwamnati ya ba da shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13 a Bauchi




Kwamitin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa domin nazarin buƙatun ƙirƙirar sababbin masarautu da yankunan hakimai da dagattai, ya ba da shawarar ƙirƙirar masarautu 13, da hakimai 2 da dagattai 113 a fadin jihar.

Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton da shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya miƙa wa Gwamna Bala Mohammed a ofishinsa da ke Bauchi.

Da yake miƙa rahoton, Akuyam ya bayyana cewa masarautu 13 da yankunan hakimai biyu da aka bayar da shawarar kafa su su ne suka cancanta daga cikin sama da buƙatu 100 da aka karɓa daga sassan jihar daban-daban.

Kwamitin, an kaddamar da shi ne a ranar 4 ga Yuli 2025, da umarnin ya duba buƙatun al’ummomi, ya tantance dalilan tarihi, al’ada da tsarin mulki, sannan ya bayar da shawarwari da za su taimaka wajen tabbatar da adalci haɗin kai da zaman lafiya a jihar.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa, kwamitin ya karɓi jimillar takardun neman masarautu 196, inda 17 suka nemi ƙirƙirar masarautu, 166 suka nemi hakimai, sauran kuma suka nemi dagattai.

Ya ce, “A ƙarshe, kwamitin yana ba da shawarar ƙirƙirar masarautu 13, sarautu 2, da yankuna 111 a faɗin Jihar Bauchi.”




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *