Malaman Kwalejin Nuhu Bamalli sun tsunduma yajin aiki

[ad_1]



Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-ker ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a Jihar Kaduna sun tsunduma yajin aiki.

Ƙungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere (ASUP) reshen makarantar ta fara yajin aikin ne daga yau Talata, 39 ga Satumba, 2025.

Ƙungiyar ta fara yajin aikin ne bayan zaman da ta yi da wakilan gwamnatin jihar, inda Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, ya buƙaci su ƙara haƙuri, yana mai alamta cewa Gwamna Uba Sani ya ba da izinin biyan buƙatunsu.

Sanarwar da Kwamared Usman Shehu Suleiman ya sanya wa hannu ta ce, “Daga Talata , 30 ga Satumba 2025 mu fara yajin aiki har sai abin da hali ya yi.”

Ya ƙara da cewa yajin aikin zai ci gaba da gudana har zuwa lokacin da suka samu amincewar gwamnati da buƙatun malaman a hukumance.

Uwar ƙungiyar ASUP ta buƙaci tafiya yajin aikin sai abin da hali ya yi ne idan gwamnatin jihar ba ta amince da tsarin albashin Kwalejojin Kimiyya da Ƙere-kere (PSS) bayan albashin watan Satumba.

Sauran buƙatun sun haɗa da aiwatar da tsarin albashi na CONPCASS/CONTEDIS ga ɗauƙacin ma’aikata a manyan makarantu mallakar jihohi da kuma ƙara yawan shekarun yin ritayar waɗanda ba malamai ba zuwa shekara 65.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *