Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na Saudiyya
Yarima mai jiran gado na Masarautar Saudiyya, Sheikh Muhammad bin Salman, ya jagoranci sallar jana’izar fitaccen malamin addini, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Muhammad Al-Sheikh.
Shafin Inside Haramain ya ruwaito cewa an gudanar da jana’izar ce a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh.
Aminiya ta ruwaito cewa za a yi masa Salatul Ga’ib a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina.
A wannan Talatar Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawar na Saudiyya rasuwa yana da shekara 82.
Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da Madina, Sheikh Abdul Rahman Sudais, sun gabatar da ta’aziyyar iyalai da ɗaliban mashahurin malamin.






