Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza
[ad_1]
Ƙasar Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan wani ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke neman a dakatar da yaki a Gaza nan take kuma ba tare da sharaɗi ba.
Daftarin kudurin na majalisar ya kuma buƙaci Isra’ila ta cire duk wani takunkumi kan kai agaji ga yankin na Falasɗinawa.
Kudurin, wanda ƙasashe 10 da aka zaɓa daga cikin mambobi 15 na majalisar suka tsara, ya kuma buƙaci a saki dukkan fursunonin aka yi garkuwa da su daga hannun Hamas da sauran kungiyoyi ba tare da sharadi ba, cikin mutunci da girmamawa.
Kudurin dai ya samu goyon bayan ƙasashe 14, sai dai Amurka ta yi amfani da karfin tuwo wajen kin amincewa da shi.
Wannan shi ne karo na shida da Amurka ke hawa kujerar-na-ki kan batun yaki tsakanin Isra’ila da Hamas tun kusan shekaru biyu da suka gabata.
Jakadiyar Denmark a Majalisar Dinkin Duniya, Christina Markus Lassen, kafin ta kada kuri’arta, ta ce, “An tabbatar da yunwa a Gaza, ba hasashe ba ne, ba jita-jita ba, an tabbatar da ita.”
Ta ƙara da cewa: “Isra’ila ta faɗaɗa hare-haren soji a birnin Gaza, lamarin da ke ƙara jefa fararen hula cikin wahala. Wannan mummunan yanayi da gazawar jin kai ne ya tilasta mu daukar mataki a yau.”
Wani rahoto daga hukumar da ke sa ido kan yunwa a duniya ya tabbatar da cewa birnin Gaza da kewaye na fama da yunwa, kuma akwai yiwuwar ta yadu.
Amurka na da al’adar kare Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai a makon da ya gabata, a wani mataki da ba kasafai ake gani ba, ta goyi bayan wata sanarwa daga majalisar da ke sukar hare-haren da aka kai Qatar, duk da cewa ba a ambaci Isra’ila a cikin rubutun ba.
Wannan mataki ya nuna goyon bayan Shugaban Amurka Donald Trump ga umarnin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayar.
Sai dai hawa kujerar-na-kin da Amurka ta yi a ranar Alhamis ya sake tabbatar da cewa Washington na ci gaba da ba Isra’ila kariya ta diflomasiyya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link