Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya
[ad_1]
Kamfanin Microsoft ya sanar da ƙwace shafukan yanar gizo na wasu kamfanoni 340 a Najeriya bayan samunsu da laifin sarrafa fasahohin kamfanin ba bisa ƙa’ida ba, musamman satar bayanan mutane.
Sanarwar da Microsoft ya fitar ta ce matakin ya biyo bayan wani umarni da wata kotu a Amurka ta bayar tun a farkon wannan wata, wadda ta bai wa kamfanin damar ɗaukar matakin ladabtarwa ga waɗanda ke amfani da fasaharsa ba tare da izini ba.
Steven Masada, mataimakin shugaban sashen lauyoyi na Microsoft da ke kula da laifukan intanet, ya bayyana cewa waɗannan kamfanoni sun ɗauki bayanan abokan hulɗarsu sama da 5,000, inda suka yi amfani da shafukan kutse domin samun bayanan sirri.
A cewarsa, ɗaya daga cikin shafukan da suka fi haddasa damuwa shi ne wani da ake kira Raccoon0356, wanda ke da mabiya fiye da 850 a manhajar Telegram. Wannan shafi ne ke bai wa wasu damar samun kayan aikin kutse don shigar bayanan sirri na Microsoft da wasu hukumomi.
Microsoft ya bayyyana Joshua Ogundipe, mazaunin Najeriya a matsayin wanda ke jagorantar wannan shafi da ke kan manhajar Telegram, kuma bai bayar da amsa a saƙon da aka aike masa ba, don ya kare kanshi game da ayyukan da kamfanin ya ce yana aikatawa.
Kamfanin na Microsoft ya ce ya gano yadda Joshua ya jima tare da ƙwarewa wajen satar bayanan mutane, inda a tsakanin 12 zuwa 28 ga watan Fabrairun wannan shekara, ya yi kutse a shafukan hukumomi sama da 2,300, mafi yawansu na Amurka.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link