Mota ɗauke da tabar wiwi ta yi hatsari a Kano, ta faɗa hannun jami’an NDLEA
[ad_1]
Hukumar Kyana da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta cafke buhuna uku da kuma kwatami 150 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 112.
Bayanai sun ce an kama kwayoyin ne bayan wani hatsarin mota da ya faru a Gadar Tamburawa da ke kan hanyar Zariya zuwa Kano.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Alhamis a Kano.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Asabar, lokacin da jami’an hukumar da ke sintiri suka ji karar hatsari tsakanin motar kirar Golf da wata babbar mota.
“Jami’anmu sun garzaya wurin don ceto mutanen da ke cikin motar Golf, inda suka cire gilashin gaban mota, taga da ƙofa don fitar da direban da fasinja,” in ji shi.
Ya kara da cewa fasinjan ya yi yunkurin tserewa lokacin da aka bude ƙofa, amma jami’an hukumar suka yi ram da shi.
“Binciken da aka yi a cikin motar ta Golf ya kai ga gano sinki 150 da buhuna uku na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 112,” in ji Muhammad-Maigatari.
A cewarsa, direban motar, wanda ke karbar magani a asibiti, ya amsa cewa shi ne wakilin wanda ya turo kayan, kuma ya taba kai irin wannan kaya a baya cikin Kano da wajen ta.
Muhammad-Maigatari ya kara da cewa direban ya amsa cewa ya bi hannun da ba nasa ba a titi don guje wa binciken NDLEA.
“Rahotannin farko sun nuna cewa direban babbar motar ya ji rauni mai tsanani. Abin da direban ya aikata ya kunshi laifuka biyu: bin hannun da ba nasa ba da ya janyo hatsari da kuma safarar miyagun kwayoyi,” in ji shi.
Jami’in ya ce hukumar karkashin jagorancin Kwamandan Jihar Kano, Abubakar Idris-Ahmad, za ta ci gaba da bin diddigin wadanda ke da hannu a safarar miyagun kwayoyin da nufin gurfanar da su a gaban kotu.
A ƙarshe, ya shawarci jama’a da su guji safarar miyagun kwayoyi, tare da bayar da rahoton duk wani motsi da bas u yarda da shi ba ke da alaka da miyagun kwayoyi ga hukumar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link