Sarkin Zazzau ya jagoranci jama’a domin murnar Maulidin bana

[ad_1]



Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya jagoranci jerin gwanon zuwa gidan Sarkin Ladanai na Zazzau a matsayin al’adar tarihi na bikin Mauludin na bana.

Bikin Mauludin na bana shi ne karo na 185 da aka shirya a hukumance da aka gudanar a Zariya.

Sarkin da ya hau kan doki ya samu rakiyar ’yan uwa na masarautar domin yin mubaya’a ga fitaccen gidan malamin addinin Musulunci, wato gidan Sarkin Ladanai.

An gudanar da bukukuwan murnar ne  don zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Manyan Malaman Addinin Musulunci sun gudanar da addu’o’i a harabar domin samar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Masarautar Zazzau da ke Jihar Kaduna da Najeriya baki ɗaya.

Abu Ladan, Sarkin Ladanai na farko da ya koyar da ilimin addinin Musulunci a makarantar da mahaifinsa Kanuri ya kafa a lokacin da ya tafi aikin hajji da ƙafa ya dawo da wasu littattafai.

Ana karanta waɗannan littafai na Musulunci a gidan duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal a matsayin wani ɓangare na tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

Waɗannan sun haɗa da yin salati ga annabi da addu’o’in zaman lafiya da wadata da ci gaban al’ummar Zazzau.

Tun daga wannan lokacin har zuwa yau, ana ci gaba da karatu da yin addu’o’in Maulidin Annabi a gidan Sarkin Ladanai.

Sarkin Zazzau, tun daga wancan zamani zuwa yanzu, ya ci gaba da halartar taron na shekara-shekara.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *