Za a gyara tarbiyar tubabbun ’yan daban Kano
[ad_1]
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci matasan da ake ribatarsu a matsayin ’yan daban siyasa da a yanzu suka tuba da su guji tashin hankali, yana tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na gyara tarbiyarsu tare da mayar da su cikin al’umma.
Gwamnan ya yi wannan alkawari ne a taron wuni ɗaya da aka gudanar tare da shugabannin rukunan ’yan daban da suka tuba a ƙarƙashin Shirin Safe Corridor.
Gwamnan, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya wakilta, ya ce: “Ba za a sake ɗaukar makami da sunan fadan siyasa ko wasu munanan dabi’u ba.
“Za mu gyara muku tarbiya, mu tabbatar kun samu ababen yi da suka dace domin samun abun dogaro da kai. Za mu karɓe ku ɗaya bayan ɗaya, mu gyara ku, mu tura ku inda kuka fi dacewa.”
Waiya ya bayyana cewa wasu daga cikin tubabbun mutanen da aka yi wa rajista a baya a cikin shirin sun riga sun rasu, inda gwamnati za ta sake gudanar da sabon aikin tantancewa domin sabunta bayanai.
Ya jaddada cewa wannan shiri ba na siyasa ba ne, yana mai cewa manufarsa ita ce kawar da matsalar ‘yan daba da sauran munanan halaye a jihar.
“Mutane da dama masu shekarunku suna yin abubuwa masu kyau. Mun fahimci cewa ba ku ci moriyar wasu shirye-shirye na tallafi ba a baya, amma yanzu mun tsaya tsayin daka domin ku,” in ji shi.
Sauran masu jawabi a yayin taron sun haɗa da Kwamandan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na Kano, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, da sauran masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Kano.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link