NASFAT ta yi gargaɗi kan yin ɓatanci ga Sahabban Annabi (SAW)
[ad_1]
Ƙungiyar Musulunci ta Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta yi kira ga malamai da mabiya addinin Islama a duniya da su guji yin kalaman ɓatanci ga sahabban Annabi Muhammad (SAW), tana mai cewa yin hakan zunubi ne mai girma kuma ya saɓa wa koyarwar addini.
Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu malamai a Jihar Kwara da wasu sassan Yammacin Najeriya sun shiga ce-ce-ku-ce saboda irin waɗannan kalamai a jan sahabban Annabi (RA).
NASFAT ta ce addinin Musulunci ya umarci a yi biyayya ga Allah da Manzonsa (SAW) tare da girmamawa da ƙaunar sahabbai baki ɗaya.
Sanarwar da kakakin NASFAT, Alhaji Shamsideen Owolabi Oseni, ya fitar ta ce,“Sahabbai ne suka fara yaɗa addinin Musulunci, suka kare shi, suka adana Alƙur’ani da Sunnah, sannan suka watsa shi ga al’ummomin da suka zo bayan su.”
Ƙungiyar ta bayyana cewa yin batanci, ƙyama ko zagin sahabbai babban zunubi ne da malamai suka bayyana tun fil azal a matsayin alamar taɓewa, wanda masu aikatawa suna iya shiga kafirci.
Ta ambaci manyan malaman Musulunci kamar Imam Ahmad, Imam al-Ɗahhaawi, Abu Zar’ah al-Raazi da Ibn Taymiyyah a cikin waɗanda suka yi gargaɗi cewa irin yin ɓatanci ga Sahabbai na girgiza tushen addinin Musulunci.
NASFAT ta ƙara da cewa ƙaunar sahabbai alama ce ta imani, yayin da ƙin su ke nuna munafunci ko kafirci. Ta ce Allah Ya yaba musu a cikin Alƙur’ani kuma Ya nuna yardarsa da su.
Kungiyar ta buƙaci malamai su kiyaye minbarorinsu daga kalaman rarrabuwar kawuna, tare da jaddada koyarwar da za ta ƙarfafa haɗin kai da gina al’umma ta fuskar addini da rayuwar yau da kullum.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link