NRC ta dakatar da jigilar jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja

[ad_1]



Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta dakatar da sufurin jirgin ƙasan da ke jigila a tsakanin Abuja zuwa Kaduna.

NRC ta sanar da ɗaukar wannan matakin ne har sai an kammala bincike kan hatsarin jirgin da ya auku a wannan Talatar.

Shugaban hukumar, Kayode Opeifa, ne ya sanar da haka jim kaɗan bayan faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa tuni tawagar masu bincike da suka haɗa da ma’aikatan NRC, hukumar binciken sufuri ta ƙasa (NSIB) da sauran hukumomin tsaro, sun isa wurin domin gudanar da bincike.

Opeifa ya yi watsi da maganganun da ake yi cewa jiragen ba su da inganci, yana mai cewa an fara mayar da kuɗin tikiti ga dukkan fasinjojin da abin ya shafa.

Ya ƙara da cewa hukumar ta karɓi fasinjojin da aka sauke a tashar Asham da kuma tashar Idu a Abuja, tare da tabbatar da cewa za a sanar da jama’a duk wani sabon mataki na gaba.

Aminiya ta ruwaito cewa a safiyar wannan Talatar ce jirgin ƙasan ɗauke da fasinjoji da ya taso daga babban birnin Najeriya zuwa Kaduna ya tuntsure yana tafe.

Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a ƙauyen Asham da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna bayan tasowar jirgin ƙasan da misalin ƙarfe 9:45 daga Abuja.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *