Kudin Da Sin Ta Samu Daga Kallon Fina-Finai Ya Zarce Yuan Biliyan 12 A Bana

[ad_1]

Bisa alkaluman da aka fitar a dandalin yanar gizo, ya zuwa ranar 3 ga watan Afrilu, kudin da Sin ta samu daga kallon fina-finai ya zarce yuan biliyan 12 a shekarar bana, inda jimilar masu kallon fina-finen ta kai miliyan 273, kana jimillar adadin fina-finan da aka nuna ta kai miliyan 39.3.

Alkaluman sun kuma nuna cewa, ya zuwa ranar 3 ga wata, kudin da Sin ta samu daga kallon fina-finai a shekarar nan ya kai kashi 23.21% na adadin da aka samu a kasuwar fina-finan kasa da kasa, wanda ya kai sahun gaba a kasuwar fina-finan duniya bisa ma’aunin nagartattun abubuwa, da samun katafariyar kasuwa, da kuma kirkira a masana’antar.

A watan Fabrairun bana, an kaddamar da shirin “Shekarar inganta tattalin arzikin fina-finai ta 2026,” wanda hukumar kula da fina-finai ta Sin da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG suka shirya. Ana sa ran shirin, tare da hadin gwiwar cibiyoyin hada-hadar kudi da dama, da dandalolin biyan kudi, da kuma dandalin nishadi, za su bayar da zunzurutun kudi akalla yuan biliyan 1.2 a matsayin tallafin kallon fina-finai ga jama’a a tsawon shekarar, inda ta hakan za a karfafa sha’awar jama’a wajen kallon fina-finai da kuma karfafa harsashin ciyar da kasuwar fina-finai gaba.

Bugu da kari, kashe kudi a bangaren kallon fina-finai ya inganta sauran sana’o’i, ciki har da cin abinci, sayayya, sufuri, da harkokin al’adu, wanda hakan ke kara kuzari mai zurfi ga tattalin arzikin da ba na shafin intanet ba. An kiyasta cewa, ya zuwa yanzu, jimillar kudin da dukkan tsarin masana’antar fina-finai ya samu ta zarce yuan biliyan 180.(Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *