Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan PDP A Kaduna, Ashiru, Zai Koma ADC A Ranar Lahadi
Tsohon dan takarar gwamnan Jihar Kaduna a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Isa Mohammed Ashiru, ya bayyana cewa zai koma jam’iyyar ADC a ranar Lahadi, 5 ga watan Afrilu.
Ashiru, ya bayyana haka ne a shafinsa na X, biyo bayan ficewarsa daga jam’iyyar PDP.
- Rikicin ADC: Lauya Ya Caccaki Kotun Ɗaukaka Ƙara
- NPA Ta Kaddamar Da Tsarin Kara Bunkasa Fitar Da Kayan Da Basu Da Nasaba Da Fannin Mai
Ya rubuta cewa: “Ni mai girma Honourable Isa Mohammed Ashiru, a ranar Lahadi 5 ga watan Afrilu, 2026 da ƙarfe 11 na safe, insha Allahu, zan yi rajista a sabuwar jam’iyyata, wato ADC.”