Kalaman Wike na barazanar harbin ɗan jarida sun tayar da kura
[ad_1]
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya tsinci kansa a tsaka mai wuya, biyo bayan barazanar harbin ɗan jarida yayin da ake tsaka da gabatar da shiri a gidan talabijin.
Wike ya yi wa fitaccen ɗan jaridar gidan talabijin na Channels, Seun Okinbaloye, barazanar harbi, lamarin da ya fusata ƙungiyoyin ’yan jarida da na kare haƙƙin ɗan Adam.
Taƙaddamar ta samo asali ne lokacin da ake gabatar da shirin Siyasa A Yau na ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu, 2026.
Okinbaloye, ya bayyana damuwarsa kan yiwuwar mayar da Najeriya ƙasa mai tsarin jam’iyya ɗaya a shekarar 2027.
Ɗan jaridar ya bayyana cewa dimokuraɗiyya tana ginuwa ne kawai idan akwai gurbin yin takara tsakanin jam’iyyu daban-daban, ba iya jam’iyya ɗaya ba.
Da yake mayar da martani yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, 3 ga watan Afrilu, Wike ya zargi Okinbaloye da nuna son kai maimakon gudanar da aikinsa bisa tsari.
Wike ya ce: “Na yi mamaki matuƙa yayin da nake kallon shirin. Idan da akwai hanyar da zan iya fasa talabijin ɗin, da na harbe shi. Ta yaya mai tambaya za ka riƙa bayyana ra’ayinsa maimakon yin tambayoyi?”
Duk da cewa daga baya Ministan ya bayyana cewa kalaman nasa ba su da nufin cutarwa, ƙungiyoyi da dama ciki har da Amnesty International da wasu haɗakar kungiyoyin fararen hula 14 sun yi Allah-wadai da kalaman nasa.
Sun buƙaci Ministan ya janye kalaman nasa tare da bai wa ɗan jaridar da gidan talabijin ɗin haƙuri.
Sun bayyana cewar irin waɗannan kalamai na iya tsoratar da kafafen yaɗa labarai tare da raunana ’yancin faɗin albarkacin baki.
A shafukan sada zumunta kuma, kalaman na Wike sun zama abun muhawara, inda wasu ke ganin sun dace da salon siyasarsa na faɗa-da gaba.
A gefe guda, wasu na ganin bai dace babban jami’in gwamnati ya furta irin waɗannan kalamai ba, domin za su iya haddasa tashin hankali.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link