An Nemi Tinubu Ya Sanya Baki Kan Rashin Biyan Fansho

[ad_1]

Kungiyar ’yan fansho ta Nijeriya (NUP), ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya tsawatar wa gwamnonin jihohin kasar, domin kawar da duk wani bashin da ‘yan fansho suke bin jihohin.

Kazalika, kungiyar ta ce; kiran nata ya zama wajibi, domin har yanzu ’yan fansho a matakin kasa da kasa, ba sa cin gajiyar sauye-sauyen da ake samu, duk da cewa; gwamnatin tarayya na ci gaba da kawo dauki ga wadanda suka yi ritaya.

  • Gwamna Uba Sani Ya Kulla Yarjejeniyar Naira Biliyan 15  Don  Inganta Wutar Lantarki  A  Kaduna
  • Sin Ta Fitar Da Mizanin Kasa Na Kyautata Nagartar Na’urar Adana Lantarki

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Godwin Abumisi ne ya yi wannan kira a lokacin da yake taya shugaban kasar murnar cika shekara 74 a duniya.

Sanarwar ta kara da cewa, “Kungiyar ‘yan Fansho ta Nijeriya (NUP), na taya mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 74 da haihuwa.

Kungiyar ta yi nuni da cewa, a yayin da ‘yan fansho a fadin kasar nan ke taya shugaban kasar murna, saboda la’akari da manufofin da suka inganta jin dadi da martabar wadanda suka yi ritaya, hakan ba zai yiwu a jihohi ba.

Da yake yin karin haske kan muhimman nasarorin da aka samu a matakin tarayya, NUP ta yi nuni da amincewa da karin kudin fansho da kimanin naira 32,000 a duk wata ga masu karbar fansho, inda ta bayyana hakan a matsayin babban taimako a cikin kalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta a halin yanzu.

Ya kara da cewa, karin “hukunci na nuna jajircewa da jin kai, wanda ya kawo saukin da ake bukata ga wadanda suka yi ritaya da suke kokawa da tsadar rayuwa,” ya kara da cewa; hakan ya sake farfado da fata a tsakanin ‘yan fansho a fadin kasar.

Kungiyar ta kuma yaba da amincewar da gwamnatin tarayya ta yi na kimanin naira biliyan 700, don kawar da wasu basukan da ake bin su a karkashin tsarin bayar da gudunmawar fansho (CPS) da kuma naira biliyan 57 ga ‘yan fansho a karkashin tsarin (DBS), tare da lura da cewa; matakin na magance basussukan da aka dade ana bin su.

Kungiyar ta NUP, ta kara amincewa da kokarin warware basussukan da ake bin ‘yan fansho, musamman ma wadanda ke cikin ma’aikatun gwamnati a karkashin tsarin fa’ida, inda ta ce; matakin ya taimaka wajen dawo da kwarin guiwar gwamnati na aiwatar da ayyukanta.

Ta kuma yaba da yadda ake ci gaba da biyan kudaden fansho na wata-wata da kuma yadda gwamnatin tarayya ta dauki matakin magance jinkiri.

“Muna kara yaba wa ci gaba da biyan kudaden fansho na wata-wata, da kuma sanya baki wajen biya a kan lokaci, wanda hakan ya nuna kyakkyawan jagoranci.”

Yayin da take yaba wa wannan kokari, NUP ta jaddada cewa; har yanzu ‘yan fansho da dama na jihohi, ba sa cin gajiyar irin wadannan sauye-sauye, don haka akwai bukatar shugaban kasa ya shiga tsakani.

“Muna kira ga girma shugaban kasa da ya yi amfani da damar da yake da ita, don samun galaba a kan gwamnonin jihohi wajen aiwatar da cikakken karin albashin da aka amince da shi ga ‘yan fansho na jihohi, ta yadda wadanda suka yi ritaya a matakin kasa baki-daya za su amfana da wadannan sauye-sauyen,” in ji sanarwar.

Kungiyar ta kuma nanata muhimmancin bin diddigin tsarin inshorar lafiya da ake shirin yi wa ‘yan fansho.

“Mun kuma sake nanata cewa, shirin Inshorar Lafiya da aka tsara na ‘yan fansho, ya na da matukar muhimmanci. Muna fatan amincewa da shi da kuma fitar da kudade, don gaggauta aiwatar da shi nan da dan wani lokaci,” in ji ta.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *