An Gudanar Da Taron ’Yan Jarida Na Bikin Al’adun Fina-Finai Na CMG A Beijing
[ad_1]
A yau Jumma’a, an gudanar da taron manema labarai na bikin al’adun fina-finai na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG a birnin Beijing. A karkashin jagorancin hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin, za a gudanar da bikin al’adun fina-finai a hukumance a birnin Ningbo dake lardin Zhejiang daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Afrilu.
Taron manema labarun ya gabatar da abubuwan da bikin ya kunsa da kuma abubuwan da suka fi daukar hankali a bikin al’adun fina-finai. Ta hanyar amfani da damar da aka samu daga tattalin arzikin ba da hidimomi ga masu sayayya, taron zai mayar da hankali kan “al’adun sinima,” “al’adun masana’antar fina-finai,” da “hade fina-finai da yawon bude ido da al’adu” ta hanyar kirkire-kirkire.
Kazalika, za a kaddamar da bangarori guda biyar a bikin don kirkirar wani abin al’ajabi na al’adun fina-finai da kuma sanya karfin CMG wajen bude ci gaban masana’antar fina-finai da sauran masana’antun da abin ya shafa.(Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link