Sojoji sun ceto yara da suka tsere daga sansanin Boko Haram
[ad_1]
Sojojin Birget na 25, waɗanda ke aiki da rundunar Forward (FOB) Azir a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno, da ke fafatawa da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun ceto wasu yara maza biyu da aka ce sun tsere daga sansanin a Dusula.
Wata majiyar soja ta shaida cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe a ranar 1 ga Afrilu bayan da shugaban ƙauyen Azir ya sanar da sojoji game da isowar yaran biyu a cikin al’umma a cikin wani yanayi da ake zargin daga hannun ’yan ta’addan Boko Haram suka kufce.
Majiyar ta ce, da samun rahoton hakan nan da nan sojoji suka garzaya zuwa ƙauyen suka kama yaran, daga baya aka kai su sansanin Sojojin na Forward don yi musu tambayoyi.
An bayyana matasan a matsayin Abuna Yammadu Kala, mai shekara 15, da Abulkaka Yammadu Kala, mai shekara 10.
A amsar tambayoyin da suka yi da farko, yaran sun bayyana cewa kwanan nan sun tsere daga sansanin ’yan ta’adda da ake zargin yana yankin Dusula.
Majiyar ta ce, yaran sun bayyana cewa sun tsere daga sansanin saboda mawuyacin hali da kuma fargabar rayukansu sakamakon yawaitar hare-haren da ‘yan ta’addan ke fuskanta daga sojojin Najeriya.
Majiyar tsaron ta ƙara da cewa, an mayar da ƙananan yaran zuwa wani wuri domin tantance bayanansu da kuma ɗaukar ƙarin matakan da suka dace don miƙa su ga hannun da ya dace.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link