Shugaban INEC Ya Yi Watsi Da Kiran Ya Yi Murabus, Ya Ce Wasa Da Hankali Ne Kawai

[ad_1]

Shugaban INEC, Farfesa Joash O. Amupitan, ya yi watsi da kiran da ADC ta yi na ya yi murabus. Ya bayyana hakan a matsayin yunƙurin karkatar da hankali daga ayyukan hukumar.

Matakin na zuwa ne bayan sukar da wasu jam’iyyun adawa suka yi wa INEC kan zargin nuna son kai. Sun buƙaci a cire shi bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da hukumar ta bi.

  • ADC Ta Nemi Shugaban INEC Ya Yi Murabus
  • 2027: INEC Ta Gabatar Wa Jam’iyyu Sabbin Ƙa’idojin Zaɓe

A cikin wata sanarwa, INEC ta ce kiran murabus ɗin ya saɓawa kundin tsarin mulki. Ta jaddada cewa sashi na 157 na kundin tsarin mulki ne ke tsara naɗi da cire shugaban hukumar.

Hukumar ta bayyana cewa ta bi umarnin kotu ne domin kauce wa matsalolin baya kamar na Zamfara da Filato. Ta ce ƙin bin hukuncin kotu kan iya jawo soke zaɓe.

INEC ta kuma ce ta dakatar da sa ido kan wani ɓangare na ADC bisa umarnin kotu. Ta jaddada cewa ba za ta tsoma baki a rikicin cikin jam’iyya ba yayin da ake ci gaba da shari’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *