Kwankwaso Ya Bayyana Dalilinsa Na Komawa Jam’iyyar ADC
[ad_1]
Kungiyar Kwankwasiyya, ta umarci mambobinta da su dunguma su shiga jam’iyyar ADC.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Dakta Habibu Sale Mohammed, mai magana da yawun kungiyar ya ce; Sanata Rabiu Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya na kasa, ya kammala shirin shiga jam’iyyar da ke neman kayar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
“Kungiyar Kwankwasiyya, na son sanar da daukacin mambobinta a fadin Nijeriya a hukumance da sauran jama’a cewa, Jagoranmu Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya shiga jam’iyyar ADC.”
“A ci gaba da yanke wannan shawara, ya yi rajista a hukumance da jam’iyyar a ranar Litinin, 30 ga Maris, 2026, a gidansa, Gidan Kwankwasiyya, Miller Road, Kano, da karfe 12 na rana.
“Saboda haka, ana umartar daukacin ‘ya’yan kungiyar Kwankwasiyya da su ci gaba da yin rijista da jam’iyyar ta ADC a yankunansu, kananan hukumomi da jahohinsu ba tare da wani bata lokaci ba.
“Wannan shawara da aka cimma, kamar yadda aka saba, an dauki matakin ne domin maslahar tafiyar da al’umma, jiharmu da kasa baki-daya, wanda hakan ke nuni da irin jajircewar da muke yi na ci gaban kimar dimokaradiyya da shugabanci nagari da kuma burin jama’a baki-daya.
“Muna jaddada cewa, dole ne a kare dimokuradiyya, kuma dole ne a mutunta muradun jama’a a koda-yaushe. Kungiyar Kwankwasiyya, ta ci gaba da dagewa da hadin kai da jajircewa wajen gina Nijeriya.”
[ad_2]
Source link