Kasar Sin Ta Dakile Matsalar Safarar Yara Da Mata

[ad_1]

Kotun kolin kasar Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, adadin yara da matan da ake sacewa tare da safararsu, ya ragu sosai a kasar da kaso 77.95 a shekarar 2025, idan aka kwantanta da matsayin koli da ya kai a shekarar 2012.

A cewar kotun, wannan na nuna an dakile yadda ake aikata wadannan laifuka yadda ya kamata.

Ta ƙara da cewa, cikin shekarun da suka gabata, kotunan ƙasar Sin sun ɗauki tsauraran matakan yaƙi da safarar ɗan adam. Baya ga haka kama wadanda ke da hannu kai tsaye wajen safarar, kotuna suna kuma hukunta wadanda suke sayen mata da yaran da aka yi safararsu, da zummar dakile bukatar dake ingiza aikata laifukan.

Bugu da kari, ana hukunta wadanda bayan sun saye matan ko yara, suka aikata karin laifuka kamar fyade ko azabtarwa ko tsare su ko cin zarafinsu. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *