Harkar tsaro a gabashin Sakkwato na ƙara taɓarɓarewa — Sanata Lamiɗo
[ad_1]
Sanata Ibrahim Lamiɗo, mai wakiltar Sakkwato ta Gabas, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara tsananta a yankinsa, inda ya ce hare-hare da satar mutane sun zama ruwan dare.
A hirarsa da manema labarai, Sanatan ya ce: “Gaskiya abin tsoro ne rayuwa a Gabashin Sakkwato. Kusan kowace rana sai an kai hari, an kashe mutane ko kuma an sace su. Muna cikin tashin hankali sosai.”
Ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da yake yi wajen ganin an kawo gyara, wasu ’yan siyasa suna kawo cikas.
Sai dai ya ce ba zai fasa jajircewa wajen ganin an ƙara yawan jami’an tsaro da sansanonin da ke Ƙananan Hukumomin Raɓah da Sabon Birni.
Sanata Lamiɗo ya yi addu’ar Allah Ya bai wa jama’ar yankin haƙuri, tare da roƙon Ubangiji ya hukunta waɗanda suke da hannu a ta’addancin.
Ya kuma yi suka ga ’yan siyasar da suke jira sai an yi mummunan lamari sannan su je jaje, maimakon su tsaya tsayin daka a magance matsalar tsaro da su.
A cewarsa, “Idan aka inganta tsaro, mutane za su iya yin noma da sana’o’insu, wannam shi ne taimakon da ya fi muhimmanci.”
Yankin Gabashin Sakkwato na daga cikin wuraren da suka fi fama da hare-hare da satar mutane, lamarin da ya kawo wa harkar noma, kasuwanci da makarantu cikas.
Mutanen yankin sun buƙaci gwamnati ta haɗa kai da sauran shugabanni domin nemo mafita game da matsalar tsaro.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link