An Shiga Ruɗani Kan Yiwuwar Kai Harin Ta’addanci Gidan Yarin Kuje
Mazauna Kuje a Babban Birnin Tarayya, suna cikin fargaba bayan rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’adda na iya kai hari gidan gyaran hali na Kuje.
Mutane da dama sun ga saƙonni a kafar WhatsApp da ke gargaɗin cewa an sanya dokar hana fita daga yamma zuwa safe.
- Ana Zargin NFF Da Shigar Da Ƙarar Bogi A Kan Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo
- 2027: Tinubu Na Son A Naɗa Shi Sarauta Ne, Ba Zaɓe Ba — Dino Melaye
Saƙonnin sun buƙaci jama’a su zauna a gida kuma su yi taka-tsantsan saboda matsalar tsaro.
Wasu daga cikin wuraren da aka ambata sun haɗa da Wowo Garage, Chibiri, Shadadi, Shetuko da Kango.
Wasu mazauna yankin sun ce lamarin gaske ne.
Sun tabbatar da ganin sojoji suna sintiri a yankin tare da umartar a rufe shaguna da wuri.
Wani mazaunin yankin ya ce an umarci ‘yan kasuwa su rufe shaguna kafin ƙarfe 7 na yamma.
Sauran sun ce wannan mataki ya biyo bayan jita-jitar cewa ‘yan ta’adda na shirin kai hari gidan yarin Kuje domin kuɓutar da ‘yan uwansu.
Sai dai ba dukkanin sassan Kuje ne ke cikin tashin hankali ba.
Wani mazaunin yankin ya ce yankinsu na cikin kwanciyar hankali, kuma har yanzu ana zirga-zirga da dare.
A gefe guda kuma, rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya ta ce ba ta da masaniya kan wata dokar hana fita ko barazanar kai hari, inda ta bayyana rahotannin a matsayin ƙarya.