Yadda ’yan sanda suka koma neman fetur a hannun masu ababen hawa a Gombe
[ad_1]
Wani al’amari da ya faru ya janyo wa rundunar ’yan sandan Jihar Gombe surutu, bayan da aka zargi wasu jami’anta da tursasa wa masu ababen hawa bayar da man fetur a matsayin fansar saɓa dokokin hanya.
Wannan dambarwa ta faru ne a daren ranar Laraba a babban titin Gombe zuwa Bauchi, daidai kusa da tsohuwar tashar mota, inda jami’an ke kafa shinge don yin bincike.
Daga cikin waɗanda lamarin ya shafa har da wani ɗan jarida da ke kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki da misalin ƙarfe 10:00 na dare.
Jami’an sun tsayar da shi bisa zargin cewa fitilar babur ɗinsa ba ta aiki, duk da cewa yana amfani da fitilar hannu domin haska hanya.
Bayan an tsare shi na tsawon mintuna 20 tare da barazanar tura babur ɗin zuwa ofishinsu, ɗaya daga cikin jami’an ya fito fili ya buƙaci ɗan jaridar da ya samo musu “galan biyu na man fetur” idan har yana buƙatar tafiya.
Yayin da ɗan jaridar ya nemi jin ba’asi a hannun babban jami’in da ke wajen, jami’in ya bayyana cewa rashin fetur da ƙarancin tallafi daga hukuma ne ya jefa su cikin wannan hali na neman agaji daga hannun jama’a domin gudanar da aikinsu.
Shaidu sun tabbatar da cewa lamarin ba iya kan mutum ɗaya ya tsaya ba, domin an ga jami’an suna tilasta wa direbobi daban-daban bayar da fetur ko kuɗi kafin a ba su damar wucewa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar bai kai ga nasara ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link