Alkaluman PMI Na Sin Sun Karu Da Kaso 50.4 Bisa Dari A Watan Maris


Alkaluman sayar da kayayyakin da masana’atu suke sarrafawa da na hidimomi na Sin, dukkanin su sun farfado zuwa matakin ci gaba a watan nan na Maris, matakin da ke nuni ga karuwar kuzarin tattalin arzikin kasar.

Wasu alkaluma da hukumar kididdiga ta Sin ko NBS ta fitar cikin wata sanarwa a Talatar nan, sun nuna yadda alkaluman sayar da kayayyakin masana’antun kasar ko PMI, ya karu da kaso 50.4 bisa dari a watan na Maris, wato karuwar kaso maki 1.4 bisa dari kan na watan Fabarairu.

Babbar masaniyar kididdiga ta hukumar ta NBS Huo Lihui, ta alakanta wannan farfadowa da gaggawar komawa ayyuka, da sarrafa hajoji a kamfanoni bayan kammala hutun bikin bazara na bana, tare da bunkasar hada-hadar kasuwa.

Kazalika, alkaluman na NBS sun shaida yadda mizanin sayayya na PMI na kamfanonin Sin a bangaren samar da hidimomi ya karu da kaso 50.1 bisa dari a watan da muke ciki, wato karuwar kaso maki 0.6 kan na watan Fabarairu. (Saminu Alhassan)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *