Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan Kano, Nasiru Gawuna Ya Fice Daga APC
Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya fice daga jam’iyyar APC. Ya bayyana murabus ɗinsa a wata wasiƙa da ya rubuta ranar 29 ga Maris, 2026.
A cikin wasiƙar da ya aike wa shugaban APC na mazabarsa ta Gawuna a ƙaramar hukumar Nassarawa, ya ce matakin nasa na raɗin kansa ne. Ya jaddada cewa ya daina zama ɗan jam’iyyar daga ranar da ya sanya hannu a takardar.
- Gwamnan Kano Ya Sauke Shehu Wada Sagagi Daga Muƙamin Kwamishina
- Bayan Cin Kamfanin META Tarar Dala Miliyan 220: Sun Yi Bazaranar Katse Kafofin Facebook, WhatsApp, Da Instagram A Nijeriya
Gawuna, wanda ya taba rike muƙamin mataimakin gwamna, ya gode wa jam’iyyar APC. Ya ce ya samu dama da gogewa a lokacin da yake cikinta.
Sai dai bai bayyana inda zai dosa a siyasance ba bayan ficewarsa. Wannan na zuwa ne yayin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Kano gabanin zaɓe mai zuwa.
Rahotanni sun nuna ana sa ran zai gana da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso. Za a gudanar da ganawar ne a gidansa da ke Miller Road a daren Litinin.