Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yusuf Tuggar ya yi murabus

[ad_1]



Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya yi murabus daga muƙaminsa, biyo bayan umarnin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ga duk masu riƙe da muƙaman siyasa da ke da niyyar tsayawa takara Zaɓen 2027 da su sauka kafin ranar 31 ga Maris.

Mai magana da yawun ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ne ya tabbatar da murabus ɗin a ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa matakin na Tuggar na da alaƙa da shirin tsayawa takarar gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar APC a Zaɓen 2027.

Ana iya tuna cewa, bayan nan Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin bisa tanadin sashe na 88(1) na Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma jadawalin da Hukumar Zaɓe ta INEC ta fitar domin shirya zaɓukan fidda gwani.

Tuggar, wanda aka naɗa minista a watan Agustan 2023, ya goge a fannin diflomasiyya da tsara manufofi, inda ya taka rawa wajen inganta dangantakar Najeriya da ƙasashen waje.

A baya, ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai daga mazabar Gamawa a Jihar Bauchi tsakanin 2007 zuwa 2011, sannan ya yi takarar gwamna a lokuta biyu.

Haka kuma, ya yi aiki a matsayin jakadan Najeriya a Jamus daga 2017 zuwa 2023, inda ya taimaka wajen ƙarfafa hulɗar kasuwanci da diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Murabus ɗinsa na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan siyasa da dama suka shiga shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *