Gawuna, Ya Yi Murabus Daga Shugabancin Hukumar FMBN Gabanin Shiga ADC
Babban jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano kuma shugaban kwamitin gudanarwa na Bankin Jingina na Nijeriya (FMBN), Nasiru Gawuna, ya yi murabus daga mukaminsa.
Murabus din Gawuna, wanda aka bayyana a cikin wata wasika mai dauke da ranar 27 ga Maris, 2026, ya fara aiki nan take. Tsohon dan takarar gwamna na APC a Kano na shirin kammala sauya shekarsa zuwa jam’iyyar ADC a ranar Talata, bayan wasu sabbin daidaituwar siyasa tsakaninsa da tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
- Tinubu Ya Ware Albashinsa Don Tallafa Wa Sojoji Da Iyalansu
- Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
A cikin wasikar, Gawuna ya ce matakin da ya dauka ya yi daidai da umarnin shugaban kasa wanda ya bukaci dukkan masu rike da mukaman siyasa dake shirin shiga siyasa, da su ajiye mukamansu kafin fara wasu harkokin siyasa gabanin zabe mai zuwa.
“Na yi murabus ne domin bin umarnin Shugaban kasa wanda ya bukaci dukkan masu mukaman siyasa su sauka bisa tanadin dokar zabe,” in ji shi.
Ya kuma bayyana godiyarsa ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa damar da aka ba shi na yin aiki, inda ya ce wannan dama babbar abin alfahari ce.
“Ina matukar godiya ga Mai Girma Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa damar da ya ba ni na yin aiki. Hakika na dauki wannan a matsayin wata dama ta ba da gudummawa wajen ci gaban FMBN da kuma kasarmu baki daya,” in ji Gawuna.