Tinubu Ya Ware Albashinsa Don Tallafa Wa Sojoji Da Iyalansu

[ad_1]

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da ƙaddamar da wani asusun tallafi na musamman domin taimakon sojojin Nijeriya, musamman waɗanda suka samu raunuka a bakin aiki, da kuma iyalan jaruman da suka rasa rayukansu yayin kare ƙasa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin bikin cikar sa shekaru 74 da haihuwa, inda ya ce shirin wata hanya ce ta girmama jarumtaka, sadaukarwa da hidimar da sojoji ke yi wa ƙasa.

  • Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
  • Gwamnatin Filato Ta Sanya Dokar Hana Fita Ta Sa’o’i 48 A Jos Ta Arewa

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya umarci Akanta-Janar na Tarayya da ya buɗe asusun musamman domin wannan shiri. An bayyana cewa asusun zai rika tallafa wa sojojin da suka jikkata, da kuma zawarawa, mazajen da matansu suka rasu, da ‘ya’yan waɗanda suka mutu a bakin aiki.

A wani ɓangare na nuna ƙudurinsa, Tinubu ya yi alƙawarin sadaukar da dukkan albashinsa tun daga lokacin da ya hau mulki a matsayin gudunmawar farko ga asusun, domin tabbatar da cewa ba a manta da waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu ba wajen samar da zaman lafiya da tsaro.

Hakazalika, ya yi kira ga gwamnonin jihohi, ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa, kamfanoni masu zaman kansu, abokansa da sauran masu fatan alheri da su goyi bayan wannan shiri. Ya ƙara da cewa za a bayyana ƙarin bayanai kan yadda asusun zai gudana nan gaba kaɗan.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *