Hakkin Ma’aurata A Kan Junansu (1)
[ad_1]
Soyayya ta gaskiya:
Dolene kayiwa matarka soyayya ta gaskiya haka ke ma dole ne a gareki, domin sai da soyayyar gaskiya za ka iya kulawa da dukkan damuwarta, ita ma sai da soyayyar gaskiya za ta iya biyayya ga mijinta.
Tsare Amana:
Wajibi ne mace ta tsare amanar mijinta, tun daga jikinta da dukiyarsa da ma duk wani sirrinta da nasa ta kula da su.
Haka kai ma wajibi ne ka tsare mata amanar dukkan gabbanka kada ka nemi mata a waje, ban da kallon mata a waje, ban da kula mata in ba wata larura mai karfi ba.
Ka kuma tsare mata sirrinta da duk wani abu da ya shafe ta.
Tausayawa juna:
Wajibi ne miji ya rika tausaya wa matarsa, saboda ita mace mai rauni ce, ga ayyukan gida ga girki da sauransu.
Haka ke ma wajibi ne ki rika tausayaw a mijinki kada ki rika dora masa nauye-nauye ki zama mai hakuri da iya abin da Allah ya azurta ku da shi.
Shige da fice:
Ba ya halatta mace ta rika fita ba tare da iznin mijinta ba, koda leke ta ta ga ko ta kofargida haramun ne ga mace.
Haka kai kuma ka kiyaye dawowa akan lokaci saboda duk mace tana so mijinta ya dawo gida akan lokaci.
Kada ta yi Azumin Nafila sai da izninsa:
saboda zai iya zuwa da bukatarsa alhali kuma tana cikin Azumi, to a nan ana iya samun matsala, ko dai a karya Azumin ko kuma shi ya shiga takura.
Duk lokacin da mijinki ya zo da bukatarsa wajibi ne ki amsa masa, haka kai ma wajibi ne idan ta zo maka da bukatarta ka amsa mata, domin ita wannan wata larura ce mai karfi, sai dai idan matar tana cikin halin al’ada.
Wajibi ne mace ta saurari mjinta idan yana magana da ita, kada ta rika ja’inja da shi da gardama.
Haka shi ma idan tana magana anaso ya nutsu ya saurare ta ya kuma yi mata magana cikin sanyin murya.
8 Kada mace ta rika raina abin da mijinta ya ba ta, haka kuma kada shi ma ya rika raina kyautatawar da take masa. 8 Mace ta rika ado da kwalli wa mijinta ta rika daukar kanta ita fa amarya ce a kullum tana zuba ado.
Kai ma ka rika yi mata ado kana kamshi ka rika zama kuma kuna hira a cikin adon ka ce na yi wannan ne saboda ke, ku yawaitawa junanku yin hakan, kai ka rika daukar kanka a matsayin ango haka ita ma.
Za Mu Ci Gaba A Mako Mai Zuwa Idan Allah Ya Kai Mu
[ad_2]
Source link