EFCC Ta Ɗauki Matakin Ƙwace Wasu Gidajen Abubakar Malami A Abuja
Jami’an (EFCC) a jiya sun rufe gidajen tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN), da ke Abuja.
Hakan na zuwa ne yayin da (ICPC) ta sanar da shirin gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban kotu a yau kan zargin almundahanar kudade.
- Saraki Ya Soki Gwamnatin Kwara Kan Ƙaruwar Rashin Tsaro
- Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)
An ga wasu jami’an EFCC sanye da kayan farar hula suna sanya alama a gidajen Malami da ke Maitama, Abuja, a ranar Litinin, lamarin da ya jawo zanga-zanga daga bangaren tsohon AGF din, inda ya tambayi sahihancin takardun da jami’an suka gabatar.
A yayin cacar baki da ta biyo baya, jami’an EFCC sun dage cewa takardun da suka kawo na umarnin kotu ne ingantattu, duk da korafin da Malami ya rika yi akai-akai.
“Ku nuna min inda aka ce ku zo ku kwace dukiyata… alhali shari’ar na gaban kotu, shin za ku iya yin hakan ba bisa ka’ida ba? Shin yana karkashin kwace dukiya ne bayan umarnin ya kare? Umarnin da aka bayar na kwanaki 14 ya riga ya kare, amma kuna zuwa ku kunyata ni.
Tun da sassafe kuna wani gidana, yanzu kuma kuna nan.
Ina umarnin da ya ba ku izinin zuwa kan dukiyata ku yi musu alama? Wannan umarnin nake son gani. Ku nuna min inda aka ce za ku iya zuwa ku yi alama a kan dukiyata. Prince (ya juya ga wani jami’in EFCC), ina umarnin? Umarnin nan ba ya bayyana a fili cewa kuna da izinin zuwa ku yi alama a kan dukiyata. Wannan lamari yana gaban kotu.
Ina umarnin kotu da ya ba ku izini? Shin kun zo ne don ku kunyata ni ba tare da dalili ba…? Ba tare da wani ingantaccen umarnin kotu ba, alhali shari’ar na gaban kotu, kuna zuwa kan dukiyata don ku kunyata ni. Haka ake yi ne? To, ku ci gaba ku yi alamar. Za mu hadu a kotu,” in ji Malami.
Sai dai an ji jami’in EFCC yana cewa, “Muna da ikon yin alama a kan dukiya idan tana karkashin dukiyar da za a kwace. Ga umarnin; na ba ka umarnin, ranka ya dade.”
A wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TB a ranar Litinin, Malami ya kara bayani kan rufe gidajensa, inda ya ce ya kalubalanci umarnin kotu da ke neman a yi kwacewar wucin gadi na dukiyoyinsa.
Ya ce, “Akwai jami’ai da suka zo sanye da kayan aiki cikakke, dauke da makamai, kuma sun kasance masu tsoratarwa da cin zarafi ga ‘yan uwana na kusa, har ma suna cewa sun zo ne don kai wasikun gayyata.
Daga karshe dai an bayar da wasikun, ba kawai a gidan da suka same ni ba, har ma da sauran gidaje na da wuraren kasuwanci na, duk an kai hari a yau (Litinin), 23 ga Maris, 2026, daga jami’an da suka ce sun fito daga EFCC.”