Arewa Maso Gabas: Buni ya buƙaci haɗin kai domin nasara a zaɓen 2027

[ad_1]



Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya buƙaci ’ya’yan jam’iyyar APC a yankin Arewa Maso Gabas, su haɗa kai domin samun nasara a zaɓen 2027.

Buni, wanda ke jagorantar jam’iyyar a yankin, ya yi wannan kira ne a taron APC da aka yi a Gombe, inda aka zaɓi sabbin shugabannin jam’iyya domin tafiyar da harkokinta a yankin.

Ya ce haɗin kai tsakanin ’ya’yan jam’iyyar yana da matuƙar muhimmanci domin ƙarfafa APC a yankin.

“Yankinmu ya taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya tun da daɗewa har zuwa yanzu,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa APC na da gwamnoni da dama a yankin tare da rinjaye a majalisar dokoki, abin da ke nuna irin tasirin da yankin ke da shi.

Buni ya yaba wa yadda aka gudanar da zaɓukan cikin gida na jam’iyyar cikin kwanciyar hankali, daga matakin gunduma har zuwa jiha.

“Yayin da muke tunkarar zaɓen 2027, dole mu manta da saɓanin da ke tsakaninmu, mu haɗa kai domin samun nasara,” in ji shi.

A nasa ɓangaren, tsohon mataimakin shugaban APC na yankin, Salihu Mustapha, ya gode wa shugabanni da mambobin jam’iyyar bisa goyon bayan da suka ba shi a tsawon lokacin da ya yi aiki.

Shi ma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya jaddada muhimmancin haɗin kai, yana mai cewa aiki tare ne zai kawo nasara a zaɓe.

Taron ya samu halartar manyan jam’iyya, ciki har da gwamnoni, ministoci da ’yan majalisu daga faɗin yankin.

Daga cikin sabbin shugabannin da aka zaɓa sun haɗa da Idris Shu’aibu a matsayin mataimakin shugaban yankin, Baba Ali a matsayin sakatare.

Sauran sun haɗa da Nitte Amangal a matsayin sakataren hulɗa da jama’a, da Hajiya Lumbi Abubakar a matsayin shugabar mata.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *