Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Ko Ana Mazuru Ana Shaho Sai Ya Yi

[ad_1]

Tun a cikin shekaru masu yawa, batun tasirin habakar tattalin arzikin Sin yana ci gaba da zama abun tattaunawa a fagen siyasa da tattalin arzikin duniya. A yayin da wasu kasashe ke kallon wannan ci gaba a matsayin barazana ga tsarin da suka saba da shi na kashin dankali, wasu na ganin lamarin a matsayin wani sabon salo na sauyin daidaiton karfi da zai kara inganta hadin gwiwar tattalin arziki da kuma samar da adalci a tsarin duniya.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin a shekarar 1949, sabuwar gwamnatin Beijing ta fuskanci kalubale masu yawa a matakin kasa da kasa. A lokacin yakin cacar baka, kasashen yamma sun dauki matakai da suka kai ga ware Sin daga wasu muhimman cibiyoyi da kasuwannin duniya.

A lokaci guda kuma, takunkumin kasuwanci da kuntatawa a fannin fasaha sun takaita damar Sin wajen shiga kasuwannin duniya da samun wasu fasahohin zamani. Wannan yanayi ya sa tattalin arzikin kasar ya kasance cikin kalubale na dogon lokaci. Amma an samu babban sauyi a tattalin arzikin Sin a karshen shekarun 1970 lokacin da kasar ta kaddamar da gyare-gyaren tattalin arziki. Manufofin da aka bullo da su sun hada da bude kofa ga waje, da habaka kasuwanci, da kuma kafa yankunan tattalin arziki na musamman baya ga shaharraren tsarin nan na “kasa daya mai amfani da tsarin mulki biyu”.

A hankali, kasar ta fara zama daya daga cikin manyan cibiyoyin samar da kayayyakin masana’antu a duniya. Sakamakon wannan ci gaba ya bayyana sosai bayan wasu ’yan shekaru. A cewar bayanai daga cibiyoyin tattalin arziki na duniya, miliyoyin mutane a Sin sun samu damar fita daga kangin talauci yayin da sabbin masana’antu da ayyukan yi suka karu.

Daga shekarun 1980 zuwa yau, tattalin arzikin Sin ya samu gagarumin ci gaba. Kasar ta zama babbar mai samar da kayayyakin masana’antu, kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da kayayyakin da ake amfani da su a kasuwannin duniya.

Haka kuma, Sin ta zuba jari sosai a manyan ayyukan more rayuwa. Misali, ta gina layukan jirgin kasa ciki har da layukan jirgi mai saurin gudu wadanda suka hade birane da dama a cikin kasar inda adadin layukan zuwa karshen 2025 ya kai tsawon kilomita 165,000, ciki har da na jirgi mai saurin gudu 50,400. Wannan tsarin sufuri ya saukaka zirga-zirga da kasuwanci a cikin gida.

Baya ga haka, Sin ta kara fadada dangantakar kasuwanci da kasashe da dama, musamman a nahiyoyin Afirka, Asiya, da Latin Amurka. A yau, kasar na daga cikin manyan abokan kasuwanci ga kasashe da dama.

Sai dai kuma, bisa wannan ci gaba, dangantaka tsakanin Sin da wasu manyan kasashe ta shiga wani sabon yanayi na gasa, musamman a fannin fasaha da kasuwanci. Ko a bara, an samu rikice-rikicen haraji tsakanin Amurka da Sin, inda aka sanya karin haraji kan wasu kayayyakin kasuwanci, ko da yake kasashen biyu suna kan tattaunawa domin maganace sabaninsu. Haka kuma an dauki wasu matakai na kuntatawa a fannin fasaha, musamman dangane da samar da kayayyakin hada sadarwar kayan laturoni “microchips”, amma duk wadannan ba su sanyaya gwiwar kasar ba.

Kasar Sin ta sha nanata kiran gudanar da gasa mai tsafta da kulla hadin gwiwa mai ciyar da al’ummomin duniya gaba, yayin da kuma take ci gaba da tafiya tare da kasashe masu tasowa wadanda ta yi wa alkawarin ba za ta taba barinsu ba. Su ma sauran hamshakan kasashen sun fahimci kyakkyawar alkiblar kasar Sin, inda shugabannin kasashe da dama ke zuwa ziyara da kuma bullo da tsarin gudanar da shawarwari kan ci gaban cinikayya da tattalin arziki. Tabbas, bisa la’akari da gwagwarmayar kasar Sin, za a iya cewa “zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho sai ya yi”. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *