An Kama Wani Mutum Kan Yi Wa Gwamna Bago Ihun ‘Ba Ruwa, Ba Wuta’ A Suleja


Rundunar ’yansandan Jihar Neja ta kama wani mutum mai shekaru 38, Hamisu Abdullahi, bisa zargin yin ihu “ba ruwa, ba wuta” yayin ziyarar Gwamna Mohammed Umaru Bago zuwa fadar Sarkin Suleja.

Kakakim ’yansandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce an kama mutumin ne saboda ƙoƙarin kawo cikas ga harkokin gwamnati a lokacin ziyarar Sallah.

  • Rikicin Gabas Ta Tsakiya Na Iya Sa A Koma Aiki Daga Gida – Dangote
  • Ministan Lantarki Ya Nemi Afuwar ‘Yan Nijeriya Kan Ƙarancin Wuta, Ya Yi Alƙawarin Yin Gyara

An kai shi sashen binciken manyan laifuka (SCID) a Minna a ranar 20 ga watan Maris.

Sai dai daga baya an bayar da belinsa yayin da ake ci gaba da bincike.

Ɗan’uwan Hamisu, Haruna Abdullahi, ya ce an sake shi da yammacin ranar Talata bayan ya shafe kwanaki biyar a tsare.

An ce Hamisu, wanda yake da yara huɗu, ya yi ihun ne a fadar Sarkin yayin ziyarar.

Akwai jita-jitar cewa gwamnan ne ya bayar da umarnin a kama shi, amma ba a tabbatar da hakan ba.

Mai magana da yawun gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce bai san da lamarin ba.

A gefe guda kuma, Cibiyar Aikin Jarida ta Duniya (IPI) a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gargaɗi gwamnan kan matakan da ka iya takura wa ’yancin aikin jarida.

Ta ce wasu abubuwa da gwamnati ke yi sun sa aikin ’yan jarida cikin tsaka mai wuya.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *